Acts 1

An Ɗauki Yesu Zuwa Sama

1A littafina na farko, Tiyofilus, na rubuta game da dukan abin da Yesu ya fara yi da abin da ya koyar 2har zuwa ranar da aka ɗauke shi zuwa sama, bayan ya ba da umarnai ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa. 3Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arbaʼin ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah. 4A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni: “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai. 5Gama Yohanna ya yi baftisma da
Ko kuwa a cikin
ruwa, amma a cikin ʼyan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”

6Saboda haka, saʼad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Israʼila?”

7Ya ce musu: “Ba naku ba ne ku san lokatai ko ranakun da Uban ya shirya cikin ikonsa. 8Amma ku za ku karɓi iko saʼad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”

9Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu.

10Suna zuba ido a bisa, zuwa cikin sararin sama yayinda yake tafiya, nan da nan, sai ga mutane biyu saye da fararen riguna tsaye kusa da su. 11Sai suka ce, “Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama.”

An Zaɓi Mattiyas Yǎ Ɗauki Matsayin Yahuda

12Sai suka koma Urushalima daga tudun da ake kira Dutsen Zaitun, tafiyar ranar Asabbaci guda daga birnin. 13Da suka iso, sai suka hau gidan sama, zuwa ɗakin da suke zama. Waɗanda suka kasance kuwa su ne: Bitrus, Yohanna, Yaƙub da Andarawus; Filibus da Toma, Bartolomeyu da Mattiyu; Yaƙub ɗan Alfayus da Siman Zilot, da kuma Yahuda ɗan Yaƙub. 14Waɗannan duka suka duƙufa cikin adduʼa, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da ʼyanʼuwansa.

15A waɗancan kwanakin Bitrus ya miƙe tsaye cikin ʼyanʼuwa masu bi (taron da ya yi kusan mutum ɗari da ashirin) 16ya ce, “ʼYanʼuwana, dole a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana tun da daɗewa ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya zama jagora ga waɗanda suka kama Yesu—  17dā shi ɗaya ne cikinmu, ya kuma yi hidima a cikin aikin nan.”

18(Da ladar da ya samu saboda muguntarsa Yahuda ya sayi wani fili; a can ya fāɗi da kā, jikinsa ya fashe, hanjinsa kuma duk suka zubo. 19Kowa a Urushalima ya ji game da wannan, saboda haka suka kira wannan filin Akeldama, da yarensu, wato, Filin Jini.)

20Bitrus ya ce, “Gama yana a rubuce a cikin Zabura cewa,

“ ‘Bari a wurinsa ya zama babu kowa;
kada kowa ya zauna a cikinsa,’
Zab 69.25

kuma,

“ ‘Bari wani ya ɗauki matsayinsa na shugabanci.’
Zab 109.8

21Saboda haka dole a zaɓi ɗaya daga cikin mutanen da suke tare da mu duk lokacin da Ubangiji Yesu yake shiga da fita a cikinmu, 22farawa daga baftisma ta Yohanna har zuwa saʼad da aka ɗauke Yesu daga gare mu. Gama dole ɗaya daga waɗannan ya zama shaidar tashinsa daga matattu tare da mu.”

23Saboda haka suka gabatar da mutane biyu: Yusuf mai suna Barsabbas (da aka kuma sani da Yustus) da kuma Mattiyas. 24Sai suka yi adduʼa suka ce, “Ubangiji, ka san zuciyar kowa. Nuna mana wanne a cikin waɗannan biyu da ka zaɓa 25ya karɓi wannan aikin manzanci, wanda Yahuda ya bari don ya tafi wurin da yake nasa.” 26Saʼan nan suka jefa ƙuriʼu, ƙuriʼar kuwa ta fāɗo a kan Mattiyas; sai aka sa shi cikin manzannin nan goma sha ɗaya.

Copyright information for HauSRK